GYARAN FATA
Fatar jiki na daya daga cikin ababen dake kare jiki bakidaya. Domin kafin komai ya taba cikin jiki sai ya taba fata. Don haka wajibi ne mu kula da fatar jikinmu.
Amfani da Cocomber da gurji da lemun tsami na cikin ababen dake kare fuska daga kunan rana tare da inganta fata.
1• A rika shafa ruwan lemun tsami da auduga kullum dare kafin a kwanta bacci bayan an wanke fuskar da sabulu. Yin hakan na magance kuraje, tare ta fitar da bakin dabo a fuska.
2•A matse ruwan dankalin turawa sannan a rika shafawa a fuska a kullum kamar sau biyu; safe da yamma sannan sai a wanke da ruwan dumi wannan hadin na haskaka fata.
3• Don dawo da hasken fatar da tayi duhu, sai a samu ayaba a bare ta sannan a kwaba ayabar sai a shafa kwabin a fuska na tsawon mintuna goma zuwa sha biyar sannan a wanke za a yi matukar mamaki Insha'Allahu.
4•Idan ana da fata mai yawan maiko, za a iya amfani da ruwan gurji da kuma ruwan lemun tsami a gauraya su sannan a rika shafawa a fuska ko jiki.
5•A samu bawon lemun zaki sannan a busar da shi sai a daka a tankade sannan a sami madara a kwaba sai a shafa a fuska na tsawon mintuna ashirin shima ya kan dawo da hasken fatar da ta dushashe.
•Za a iya shafa rose water (Ma'u-wardi) a fuska domin samun fuska mai sheki da kuma sulbi.






No comments:
Post a Comment