Tuesday, May 19, 2020
Friday, May 15, 2020
MAGANIN ZUBAR JINI YAYIN AL'ADA
KO KANA BUKATAR YARANKA SU TASO DA KAIFIN BASIRA ?
Thursday, May 14, 2020
MAGANIN LIMONIYA MAI CUTARWA
BINCIKE NA MUSAMMAN AKAN NAMIJIN GORO DA AMFANONINSA GA LAFIYAR DAN-ADAM
MAGANIN SANYIN MATA KO INFECTION
CIWON MARA MAI TSANANI LOKACIN AL'ADA
CIWON MARA MAI TSANANI LOKACIN AL'ADA
Ciwon Mara wata babbar lalurace da take addabar al'umma musamman mata ayau, wanda wasu lokuta hakan yakan kasancene sanadiyyar canzawar lokutan haila, amma Mafi muni shine idan an canza lokacin zuwan haila da gangan ta hanyar yin allura domin a janyo haila ko kuma a nisanta kwanakin zuwanta saboda wasu dalilai.
Maccenda ko mijinda matarsa ko yarsa take fama da wannnan lalurar yayi amfani da waddannan gagun gunan insha Allah zaa samu waraka.
1. Asamu man Hulba, man Habbatis sauda, cokali goma goma.
2. Ruwan khal cokali goma sai ahada da ruwan zafi rabin kofi asha sannan ayi tsaye kamar minti goma sha biyar.
Za'asha wannan kwana uku kamin zuwan jinin haila.
GARGADI
Kar mace mai ciwon ulcer wato gyanbon ciki tayi amfani da wannan maganin haka mace mai ciki itama kar tayi amfani da wannan maganin.
GYARAN FATA
MAGANIN CIWON SANYI NA MATA DA WANDA MAZA SUKE DAUKA WAJEN SADUWA DA IYALAN SU WATO INFECTIONS
MAGANIN CIWON SANYI NA MATA DA WANDA MAZA SUKE DAUKA WAJEN SADUWA DA IYALAN SU WATO INFECTIONS
YANDA ZA'A HADA MAGANIN
1- A samu namijin goro guda biyar
2- a samu citta mai mai yatsu guda 4, ko 5
3- a samu tafarnuwa guda 3 a ko 4 ajajjaga su.
4- lemon tsami guda uku
Sai ayanka su kanana Kuma a jajjaga su,
Shikuma lemon tsamin ayanka shi amatsa ruwan acikin tukuya Kuma ajefa bawon aciki atafasa su dukka,
Atace kafin asha, idan kuma babu dadin sha to sai azuba zuma za'asha dan yayi dandano,
Asha Kofi daya da lokacin sahur, bayan buda bakima asha kofi day, zuwa sati biyu.
Idan kuma ba'a watan azumi bane, to sai asha rabin kofi sau uku 3 a Rana na tsahon sati 2.
Insha Allah za'a warke asamu lafiya da izinin Allah.
Kuma wannan hadin yana maganin gonoria, da sanyi mai rike gabobi da sauransu.
MAGANIN CIWON IDO WANDA YA GAGARA
MAGANIN CIWON IDO WANDA YA GAGARA
Idan mutum ya kamu da ciwon ido kowanne irinhmm ciwon idone, Ko da irin Wanda yake dishi-dishi din nan ne, ko Qaikayin ido, da sauran cututtukan da duka shafi ido.
YANDA ZA'A HADA MAGANIN
Asamu zuma mai kyau marar gauraye arika yin tozali da ita(sawa aido kamar kwalli) kafin akwanta barci. sannan da safe ma amaimaita.
Kuma marar lafiyan zai rika shan cokali Daya🥄 na Zumar akullum.
TSAWON KWANAKIN AMFANI DA MAGANIN
Za’ayi haka har tsawon kwana bakwai zuwa kwana goma Sha hudu. Insha Allahu za’a warke tas da izinin Allah.
BINCIKE NA MUSAMMAN AKAN TUMATIR
MAGANIN CIWON MAKOGORO
MAGANIN CIWON MAKOGORO
Don magance matsalar ciwon makogoro sai abi wadanan matakai kamar haka;
YANDA ZA'A HADA MAGANIN
Asamu saiwar sanya da citta da Kanumfari da kimba da na'a-na'a, sai ahadasu waje guda adaka atankade atafasa cokali biyu acikin ruwa kofi daya atace asa zuma a matsa lemun tsami agarwaya.
AWUN SHAN MAGANIN
BABBA;- yasha kofi daya sau biyu arana zuwa kwana bakwai.
YARO;- yasha rabin kofi sau biyu arana zuwa kwana biyar.
GARGADI
kar mace mai ciki tayi amfani da wannan maganin, haka mai fama da ciwon gyanbon ciki wato ulcer shima kar yayi amfani da wannan maganin.
MATSALOLIN DA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI HUNHU
MATSALOLIN DA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI HUNHU*
Akwai matsaloli da cuttuka dayawa da suka shafi hunhu, kama daga kan ciwon daji na hunhu wato ( lung cancer ) Da asima, da nimoniya da mura mai tsana ko tari mai tsananin gaske, da matsalar shakewar numfashi da sauransu.
YANDA ZA'A HADA MAGANIN
Asamu wadanan mahadai kamar haka;-
1. Garin Habbatus-sauda 2. Kimba
3. Na'a-na'a
4. Citta
5. Sassaken marke
6. Kanumfari
7. Kusdul-hindi
8. Girfat
9. 'ya'yan bagaruwa
10. Masoro
11. Ganyen runhu
12. Garin zaitun Sai ahadasu waje guda adaka atankade atafasa cokali uku acikin ruwa rabin lita atace asa zuma agarwaya.
*AWUN SHAN MAGANIN*
*BABBA:-* Yasha kofi daya sau biyu arana zuwa kwana bakwai.
*YARO:-* Yasha rabin kofi sau biyu arana zuwa kwana uku.
*MACE MAI CIKI:-* kar mace mai ciki tayi amfani da wannan maganin har sai cikinta ya kai wata uku zuwa sama, sai ta Sha rabin kofi sau daya arana zuwa kwana hudu.
*AMFANIN MAGANIN*
1. Yana maganin ciwon daji na hunhu wato lung cancer.
2. Yana maganin ciwon makogoro.
3. Yana maganin mura. 4. Yana maganin shakewar numfashi.
5. Yana naganin nimoniya.
7. Yana maganin mugun tari.
8. Yana maganin dattin taba da goro.
9. Yana maganin asima da sanyi.
10. Yana maganin infection na maza da mata.













































