Breaking

Thursday, May 14, 2020

BINCIKE NA MUSAMMAN AKAN NAMIJIN GORO DA AMFANONINSA GA LAFIYAR DAN-ADAM


BINCIKE NA MUSAMMAN AKAN NAMIJIN GORO DA AMFANONINSA GA LAFIYAR DAN-ADAM

 

(1) YANA KASHE DAFIN MACIJI:
Namijin goro yana kashe dafin cizon maciji, idan maciji ya ciji mutum to sai a girba namijin goro guda daya tare da danyar citta ajika atace amatsa lemun tsamina aba si ya sha insha'Allahu nan take zai kashe dafin cizon macijin.

(2) YANA KASHE MACIJI:
Ana shanya namijin goro ya bushe sai a daka, a barbada a wajen da ba a so macijin ya shiga, idan macijin ya ketara wannan garin namijin goron to nan take zai mutu da yardar Allah.

(3) YANA KASHE GUBA:
Duk wanda ya sha wata guba da gan-gan ko bisa kuskure, to asamu namijin goro guda uku akirba ajika da ruwa kofi daya abashi ya hanye, insha'Allah zai amayar da gubar da ya sha, ko ta lalace acikinsa da izinin Allah.


Ana yayyanka namijin goro a jika abarshi ya kwana da safe kafin aci komai sai  rika sha zuwa kwana bakwai, insha'Allah duk wata gubar da ke jikin mutum za ta fita.

(5) YANA KARA KARFI:
Ana cin namijin goro tare da citta saboda da karin karfi ga masu iyalai 'yan mintuna Kafin a je ga iyalan.

(6) YANA MAGANIN CIWON GABABUWA:
Cin Namijin goro na magance matsalar ciwon gabobi, kamar yawan gullewa da zugi, yana kuma rage kowane irin radadin mai tsanana da ikon Allah.

)
Yawan cin namijin goro na kashe kwayoyin cutar da ake dauka wajen saduwa wato STD.

(8) YANA INGANTA LAFIYAR HUNHU:
Cin namijin goro goro na kara lafiyar hunhun dan-Adam.

(9) YANA GINA GARKUWAR JIKI:
Namijin goro na da kaso mai yawa na sinadarin 'antioxidant' Wanda ke da muhimmancin gaske wajen yakar kwayoyin cututtuka da kuma sake gina garkuwar jikin dan-Adam.

(10)  YANA MAGANIN ZAZZABIN CIZON SAURO:
Namijin goro rigakafi ne daga kamuwa da zazzabin cizon sauro wato maleriya.

(11) YANA INGANTA LAFIYAR IDANU:
Cin namijin goro na kare idanu daga makancewa da yardar Allah.

 (12) YANA KASHE GYAMBON-CIKI
Mai wannan larura idan yana cin namijin goro tare da dabino to! insha'Allah zai warke.

No comments:

Post a Comment